Mun tafka asarar £115.5m a kakar wasan 2021/22 – Manchester United | Aminiya

Mun tafka asarar £115.5m a kakar wasan 2021/22 – Manchester United

    Sani Ibrahim Paki

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da ke Ingila ta sanar da tafka asarar Yuro miliyan 115.5 a kakar wasan 2021/22.

Sai dai kungiyar, wacce ta sanar da hakan ranar Alhamis, ta ce kudaden shigarta sun karu zuwa Yuro miliyan 583 sakamakon sassauta dokokin kariyar COVID-19.

Kazalika, United ta ce a kakar wasannin wacce ta kare ranar 30 ga watan Yunin 2022, bashin da ake bin ta ya karu zuwa kashi 22 cikin 100.

Yanzu dai darajar kungiyar wacce ta taba zama zakara a gasar Cin Kofin Ingila har sau 20, ta tashi daga Yuro miliyan 419 a 2021, zuwa Yuro miliyan 514 a bana.

United dai ta alakanta karuwar bashin da faduwar da darajar Yuro ya yi a kan Dalar Amurka, lamarin da ya kara yawan kudaden.

Sauran abubuwan da suka jawo wa kungiyar tafka asarar sun hada da biyan ribar Yuro miliyan 33.6 ga masu hannun jari a cikinta da kuma biyan kudaden sallama ga tsohon Kocinta, Ole Gunnar Solskjaer wanda ta dakatar a watan Nuwamban 2021.

Amma kungiyar ta ce babban abin da ya jawo mata asarar shi ne karuwa kudaden da take biyan ’yan wasanta zuwa Yuro miliyan 384.2.