Mun yaba da rufe kan iyakoki Najeriya | Aminiya

Mun yaba da rufe kan iyakoki Najeriya

    Isah Ramin Hudu Hadeja

Hakika rufe kan iyakoki da gwamnatin Shugaba Buhari ta yi domin inganta tattalin arzikin kasar abin yabawa ne sosai. Duk da cewa wannan mataki ya jawo wa Shugaban Kasar suka da caccaka a wajen al’ummar kasar nan, amma kamar likita ne, yana jinya ana kuka da shi. Sai daga baya ne za a fahimci alherin da ke tattare da wannan mataki. Sai dai muna kira ga Shugaba Buhari don Allah Ya samo wa talakawan da suka zabe shi, wata hanya da za ta rage musu radadin tsadar rayuwa, sakamakon wannan mataki da aka dauka.

Domin a zahiri talakawa na jin jiki, wanda hakan ke jawo musu tsokana daga wadansu makiya Najeriya da kullum burinsu su ga gazawar gwamnati.

Da fatar Allah Ya kawo mana karshen halin da damuwa da muka shiga, Ya wadata kasarmu Najeriya da al’ummarta.

 

Daga: Isah Ramin Hudu Hadeja. 08060353382.