✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mun yi Sallah cikin kunci saboda rashin albashi – Ma’aikatan Kano

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin ta yanke wa ma’aikatan albashinsu a watannin baya

Yayin da al’ummar musulmi suka wayi gari da farin cikin bukukuwan Sallah a fadin duniya, ma’aikatan gwamnati a Jihar Kano sun ce lami suka yi ta saboda rashin samun albashinsu na watan Afrilu da ya kare tun ranar Juma’a.

Wasu ma’aikatan da muka tattauna da su sun bayyana mana yadda hakan ya jefa su a halin tsaka mai wuya, musamman kasancewar da dama daga cikinsu ba su samu yi wa kai da iyali dinkunan Sallah, da Zakkar fidda kai, har ma da Tuwon Sallah ba.

Wani ma’aikaci da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce suna cikin yanayi mara dadi, saboda rashin kudi, kuma abubuwa da dama ba su samu yi ba.

“Mun yi Sallah cikin rashin walwala, yara na ta kukan rashin nama a abinci ranar Sallah, kuma gaskiya ba a yi mana adalci ba,” inji wata ma’aikaciya a Hukumar Ilimi ta Kano mai suna Hajiya Samira.

Shi kuwa wani ma’aikacin mai suna Ahmad Tijjani Muhammad ya ce, “Gaskiya a sallar nan sai dai godiyar Allah saboda mu ma’aikata ba mu samu dama mun yi abubuwan da suka dace ba saboda Gwamnatin Jihar Kano ba ta biya albashi ba.

“Wannan ya sa muna cikin wani yanayi mara dadi matuka, saboda abubuwa da yawa da suka kamata a yi duk ba a yi ba, saboda babu.

“Ina so na yi amfani da wannan dama na yi kira don Allah Gwamnatin Kano ta gaggauta biyan albashin wannan wata na Afrilu da ya kare, ko babu komai za a samu a yi abin da ake kira Damage Control [rangwamin barna] tun da lokaci ya riga ya kure.”

Haka kuma shi ma wani mai suna Sani Muhammad Idris ya ce, “Gaskiya duk wani ma’aikaci na Jihar Kano da kuma na Kananan Hukumomi gaba daya kowa yana cikin wani irin yanayi mara dadi.

“Muna cikin damuwa kwarai da gaske, musamman yanayin da ake ciki na takura saboda talauci ya yi wa al’umma katutu, abin da za su ci su sha ma ya zama sai dai Inna lilLahi wa inna IlayHi raji’un.

“Kuma a daidai irin wannan yanayin da iyalai suke da bukatu musamman yara da mata da sauransu, kowa yana da bukatu wanda yake sun zama wajibi a ce an biya musu domin yalwata musu da kuma sa musu farin ciki da jin dadi.

“Amma yau wannan Sallar ga shi ta zo mana lami, babu abin da za mu iya cewa sai dai mu fawwala wa Allah komai, amma babu shakka ma’aikata suna cikin wani irin hali mara dadi kwarai dagaske.

“Muna kuma fatan Allah Ya kawo mana mafita daga gare Shi.

Wannan matsala dai ta rashin albashin ta shafi tattalin arzikin Jihar, inda wasu ’yan kasuwa suka bayyana yadda hakan ya sanya kayan abinci da nama, da ma sutura domin kayan sallah suka yi bandaro a kasuwanni saboda babu masu siya.

Wani dan kasuwa ya ce, “To a gaskiya a matsayina na mai siyar da kaji an kuntata min, saboda na zuba kimanin kaji 50 da doriya kuma yanzu yau sallah amma ina gaya ma ban gama sayar da kaji na ba, akwai saura a kasa.

“Saboda haka wannan gwamnati da bata biya albashi ba, ta kuntata mana saboda babu kudi a hannun mutane. Mutane suna cikin wahala, an yi sallah lami, babu kudi, babu abinci, babu sabuwar sutura, babu kaji, babu nama.

“Ko ’yar watandar da muka saba gani ana yi ga shi nan ko ina kamas babu jini saboda ba a yi yanka ba, gaskiyar magana wannan gwamnati tana kara wa mutane azaba bayan wadda suke ciki.

“Muna kira ga mai girma gwamna ya tausaya ma’aikata ya biya su albashi, saboda mu ma yan kasuwa mu samu wadanda za su yi mana ciniki, saboda dole sai kudi sun shigo hannun maaikata sannan za su shigo kasuwa su yi siyayya, kudi su jujjuya. Allah Ya sa mu dace.

Wannan dai na zuwa ne duk da gwamnatin ta rage wa ma’aikatan albashi a baya, saboda a cewarta ba za ta iya biya bisa tsarin mafi karancin albashi na N30,000 ba.

Aminiya ta tuntubi Kakakin Gwamnan Kano, Abba Anwar dangane da lamarin, inda ya ce wannan batu Ofishin Shugaban Ma’aikatan Kano ko kuma Kwamishinan Kudi na Jihar ne suka fi dacewa su yi magana a kai.