✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun yi wa mutum miliyan 2.3 rajistar katin zabe a Arewa maso Gabas – INEC

INEC ta ce akwai yiwuwar kara samun adadin mutane da za su fito yin rajistar.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta yi wa mutum miliyan biyu da dubu 300 rajistar katin zabe a yankin Arewa Maso Gabas.

Kwamishinan hukumar da ke kula da yankin, Dakta Baba Bila, ne ya bayyana lokacin da yake jawabi a Yola a ranar Laraba bayan ya kai ziyarar gani da ido a wasu kananan hukumomin jihar Adamawa.

Kwamishinan ya yaba wa ofishin Adamawa da ke karkashin Barista Kassim Geidam, bisa tsayuwar daka wajen gudanar wajen gudanar da aikin.

Bila ya ce, “Alkaluman mutanen da aka yi wa rajistar sun kai miliyan biyu da dubu 300, amma za a iya samun maimaicin wasu katinan, kuma idan har an samu, za a cire su daga cikin wadanda aka lissafa,” inji Bila.

Da yake bai wa ‘yan Najeriya shawara kan halin yin abu a kurarren lokaci, Kwamishinan ya bukaci masu kada kuri’a da su yi amfani da isasshen lokacin da aka ba su don muhimmancin da yake da shi ga kasa.

Ya kuma yi nuni da cewa akwai wasu katunan zabe da ke a wuraren rajista, inda ya yi kira ga masu kada kuri’a da su fara tantance katin kafin su fara yin sabuwar rajistar.

“Aikin da aka yi a Adamawa ya yi nasara sosai kuma ya gamsar da jama’a da yawa, mun ga yadda aka sa ido a kan aikin. Sai dai shawarar da zan bayar ita ce jama’a su daina yin rajista fiye da sau daya saboda ba za ta yi musu amfani ba, domin daga karshe za a cire su baki daya.”

Bila ya kara da cewa “Za mu ci gaba da bayar da shawarwari domin karfafa gwiwar mutane su fito su karbi katinansu a kan lokaci.”

Wasu daga cikin masu kada kuri’a da Aminiya ta zanta da su, sun yaba da yadda ake yin rajistar a jihar tare da yin kira da a kara tsawaita lokaci domin bai wa ‘yan Najeriya damar yin katin.