✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna roka wa Najeriya shugaba kamar Buhari a 2023 —Umahi

Gwamnan Ebonyi ya roka wa Najeriya samun shugaba 'mai tausayi' kamar Buhari.

Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya roki Allah Ya sake ba wa Najeriya shugaba mai “tausayi” kamar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

Gwamna Umahi ya yi wannan fata ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Litinin.

Sai dai ya ja hankali cewa a yanzu lokaci bai yi ba na fara batun zaben 2023 domin yin hakan zai dauke hankalin shugaban kasa da gwamnoni daga ayyukan da ke gabansu.

A cewarsa, duk da haka, jam’iyyu daban-daban a yankin Kudu maso Gabas na aiki a cikin gida domin tabbatar da ganin ’yan takararsu na shugaban kasa sun fito daga yankin.

Da aka tambaye shi ko manyan jam’iyyun APC da PDP za su tsayar ’yan takarar shugaban kasa daga yankin, Umahi ya ce: “Ni dai abin da na fi mayar da hankali a kai yanzu shi ne kammala manyan ayyukan da na fara.

“Idan ya rage saura shekara daya in kammala wa’adina kuma zan waiwayo kan harkar siyasa — wato daga ranar 29 ga Mayu, 29 2022.

“Ina ganin wannan shi ne matsayin sauran gwamnonin yankin Kudu maso Gaba, musamman ma ’yan jam’iyyar APC.

“Matsayata ita ce akwai mutane a cikin waddannan jam’iyyu da suka dukufa wajen tallata dacewar shugaban kasa ya fito daga yankin Kudu maso Gabas a 2023.”