✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muna binciken mijin da ya kashe matarsa kan burodi —Gwamnatin Anambra

Gwamnatin ta ce lokaci ya yi da za a daina cin zarafin mata da sunan aure.

Gwamnatin Jihar Anambra ta ce za ta fara gudanar da bincike kan zargin yadda wani mutum da kashe matarsa a kan yankan burodi.

Kwamishinar Mata da Walwala ta jihar, Misis Ify Obinabo ce, ta bayyana hakan a ranar Laraba a Awka, bayan ganawarta da mahaifiyar mamaciyar.

“Gwamnati ba za ta yi shiru kan wannan lamari ba, dole za a gudanar da bincike tare da kammala shi cikin kankanin lokaci,” in ji ta.

Aminiya dai ta ruwaito yadda wani bidiyo ya karade kafafen sada zumunta, wanda a ciki aka nuna wani mutum yana jibgar matarsa a kan burodi, lamarin da ya yi ajalinta.

Kwamishinar ta ce ya kamata mata su fahimci cewa lokaci ya yi da za su fito fili don yaki da cin zarafi da ake musu a gidajen aure.

Sai dai mahaifiyar marigayiyar, Misis Cordelia Anene, ta yi zargin cewar surukin nata ya tsere bayan aikata laifin.

Ta roki gwamnati da ta yi bincike don yi wa ’yarta adalci.

Anene ta ce, “Mijinta ya yi ajalinta saboda ta cinye burodin da ya saya wa ’ya’yansa.

“Ransa ya baci saboda lokacin da yaran suka bukaci cin burodin suka ga babu shi ne ya hada kanta da jikin mabudi ya kuma bar ta cikin mummunan yanayi.

“Kwanaki kadan da faruwar lamarin aka kwantar da ita a Asibitin Koyarwa na UNTH da ke Inugu, wanda a nan likita ya tabbatar da rasuwarta.”

Ta ce sun mika gawar don gudanar da bincike, amma abun mamaki dan sandan da ke kula da lamarin, ya bukaci da su janye karar da suka shigar.