✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muna da hujjoji kan cewa Tinubu tsohon mai laifi ne – Dino Melaye 

Dino Melaye ya ce APC ce ta shirya komai don yi wa Atiku yarfe irin na siyasa.

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, Sanata Dino Melaye, ya ce akwai hujojjin da ke nuna laifin da ake zargin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da aikatawa.

Melaye, ya mayar da martani ne kan zargin da Mike Achimugu ya yi wa Atiku yayin wata hira da gidan talabijin na Channels.

Achimugu ya yi ikirarin cewa shi ne tsohon mai taimaka wa Atiku, dan takarar Shugaban Kasa na PDP.

Ya kuma zargi Atiku da yin amfani da motoci na musamman wajen wawure wasu kudade lokacin da yake matsayin mataimakin Obasanjo tsakanin 1999 zuwa 2007.

Amma da yake mayar da martani, Melaye ya ce, “Ba Atiku Abubakar kadai ne tsohon mataimakin shugaban kasar tarayyar Najeriya ba. Shi din (daya daga cikin) mafi shaharar ‘yan Najeriya a yau a duniya. Mutane suna haduwa da shi a kan tituna a kullum.

“Mun yi tafiya a titunan Landan. Mutane suna tare shi don daukar hoto da shi. Don ka yi hoto da Atiku Abubakar, ka yi mu’amala da shi na wasu mintuna sai ka ce kai ne mai taimaka masa. Wannan ba abin da za a yarda da shi ba ne.

“Abin da nake cewa a zahiri shi ne duk wata magana da ya yi jam’iyyar APC ce ta dauki nauyinsa don haifar da rudani.

“Festus Keyamo ya rubuta wa kotu kokensa kan bukatar a kama Atiku.

“Mutumin da ke bukatar murabus shi ne mutumin da ba shi da lafiya. Kundin tsarin mulkin kasar nan ya ce idan ka zama shugaban Tarayyar Najeriya dole ne ka kasance cikin koshin lafiya.

“Tinubu ba shi da lafiya. Muna da shaidar laifukansa. Muna da shaidar tuhumarsa da ake yi. Me zai yi idan ya zama Shugaban Kasa?”

Idan za a iya tunawa dai wani sauti ya karade kafafen sada zumunta inda aka ji wata murya irin ta Atiku tana bayanin yadda aka yi wata badakalar kudade.

Hakan ya sa Festus Keyamo ya aike wa da EFCC da ICPC takarda kan bukatar cafke Atiku.