✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna dab da shiryawa da Kwankwaso —Ganduje

Ganduje ya ce ’yan jagaliya da ba sa son ganin shi tare da Kwankwaso ne ke rura wutar rikici a tsakaninsu

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce a shirye yake ya shirya da tsohon mai gidansa kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Ganduje bayyana haka ne a hirarsa da gidan rediyon Farnasa inda ya ce ’yan jagaliyar siyasa da ba sa son ganin shi da Kwankwaso a inuwa daya ne ke rura wutar zaman doya da manja a tsakaninsu a halin yanzu.

“Ka san akwai mutanen da sun saba tayar da kura, amma muna kokarin ganin mun sha gabansu mun sasanta.

“Wannan ba bakon abu ba ne a siyasa kuma in Allah Ya yarda zai zama tarihi.

“Kowa ya san sulhu shi ne abin da ya fi alheri. Muna addu’a Allah Ya ba wadanda suke kokarin sasanta bangarorin su yi nasara,” inji shi.

“Mu dai a shirin muke mu zo a sasanta, ba wai mun ki ba ne. Kamar yadda na ce, akwai mutane daga bangarorin biyu da ke iza wutar. Amma duk da aka sanya zurfin tunani a cikinsa, to za a shawo kansa.”

Idan ba a manta ba a ranar Talata, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kai wa Sanata Kwankwaso ziyarar ta’aziyyar rasuwarsa dan uwansa, Inuwa Musa Kwankwaso,  a gidansa da ke unguwar Bompai residence.

Ziyarar da ta haifar da maganganu a tsakanin masu sharhi da ’yan siyasa a fadin Jihar Kano.

A lokacin ziyarar, Kwankwaso da mukarrabansa ne suka tarbi Ganduje da ’yan rakiyarsa da suka hada da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati da kwamishinoni da manyan jami’an gwamantin jihar.

A lokacin ne Sanata Kwankwaso ya gayyaci gwamnan zuwa wurin kabarin mahaifinsa, Marigayi Musa Saleh Kwankwaso, da ke gidan nasa, inda a nan ma aka yi wa mahaifin addu’a.

Manyan ’yan siyasar biyu sun shafa rabin awa a tare, kafin bakin su koma bayan Kwankwaso da Ganduje sun yi wata ganawar sirri a tskaninsu.