✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna maraba da kowa zuwa jam’iyyar NNPP —Kwankwaso

Kwankwaso ya ce kofa a bude ta ke ga kowa a jam'iyyar NNPP mai kayan marmari.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce kofa a bude take ga duk mai son sauya sheka zuwa jam’iyyar, ciki har da wadanda suke da sabanin ra’ayi na siyasa.

Kalaman na Kwankwaso na zuwa ne bayan rade-radin da ake na cewar tsohon Gwamnan Jihar, Malam Ibrahim Shekarau na shirin sauya sheka daga APC zuwa jam’iyyar ta NNPP.

Kazalika, tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Kabiru Alhassan Rurum, wanda ya fice daga APC da tsohon dan majalisar tarayya, Kawu Sumaila da ke shirin ficewa daga jam’iyyar, na shirin komawa NNPP.

Sauya shekar tasu ya biyo bayan mara baya da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi ga Mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna kan takarar gwamnan jihar.

Da yake magana a wani shirin siyasa, da daya daga cikin gidajen rediyon Kano, Kwankwaso ya ce NNPP na bukatar sabbin mabiya da za su shiga tafiyar jam’iyyar.

“Bayan farfado da jam’iyyar nan, muna bukatar wadanda muka sani da ma wadanda ba mu sani ba su shigo cikinta. Har wadanda muke da sabani su shigo mu yi tafiya tare. Ba za mu tsaya iya abokanmu ba. Hakan ba zai taimaki jam’iyyar a siyasance ba.

“Muna farin ciki wannan babbar jam’iyya tana daukar hankali manyan mutane. Muna maraba da duk wanda zai sa mu ci gaba a Najeriya. Muna da shiri ga Najeriya. Muna son cire Najeriya daga kangin talauci, matsalar tsaro, bunkasa tattalin arzikin kasa da ya durkushe,” a cewarsa.

Kwankwaso, ya ce kofa a bude ta ke ga ’yan bakwai wato G-7, tsagin Sanata Shekarau da ke shirin ficewa daga APC, bayan samun takun-saka da Gwamnatin Jihar kan shugabancin jam’iyyar.

Har wa yau, Kwankwaso ya ce NNPP za ta kafa gwamnati a Jihar Kano, sannan ta bunkasa Jihar.

“Kowa a Kano ba ya farin ciki da yadda abubuwa ke tafiya. Abun bakin ciki ne yadda aka lalata al’amura a shekaru bakwai da suka gabata.

“Muna son daidaita al’amura. Da yardar ubangiji za mu kawo canji a 2023 kamar yadda muka yi a 2015. Mutanenmu za su dawo su dora daga inda suka tsaya, inji shi.