✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mako mai zuwa muke sa ran ASUU ta dawo aiki —Gwamnati

Ministan Kwadago ya ce kowane bangare ya tafi da farin ciki bayan tattaunawar gwamnati ta malaman jami'a

Gwamnatin Tarayya ta ce tana sa ran a makon nan da za a shiga kungiyar malaman jami’a ta ASUU za ta janye yajin aikin ta tsawaita.

Gwamnatin ta ce tana kyautata zaton tattaunawar da ta yi da ASUU za ta haifar da kyakkyawan sakamako, kamar yadda kakakin ma’aikatar kwadago, Olajide Oshundun, ya sanar a ranar Juma’a.

Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya ce, “Mun tattauna ta yadda kowa ya tafi yana murna. Mun cim ma matsaya kuma muna fatan nan da mako mai zuwa, komai zai daidaita,” a cewar sanarwar.

Ya kuma ce, “Mun yi muhimmiyar tattaunawa; mun yi duba kan al’amuran da ba a so kuma mun yi yarjejeniya, kuma hakan ya gamsar da duk wanda ya halarci taron.”

Sanarwar ta ce Ngige bayyana hakan ne a tattaunawarsa da ’yan jarida bayan kammala wata tattaunawa da gwamnati ta yi da ASUU a Fadar Shugaban Kasa.

ASUU da Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a ta Najeriya (SSANU) da sauran kungiyoyin kwadago na jami’o’in gwamnati, sun shiga yajin aiki sakamakon gazawar Gwamnatin Tarayya wajen biyan bukatunsu.