✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muna sa ran daminar bana za ta yi albarka a Jihar Kaduna – Kwamishinar Gona

Kwamishinar Ma’aikatar Gona ta Jihar Kaduna, Halima Lawal ta ce tana da yakinin daminar bana za ta yi albarka duk da barkewar cutar Kurona da…

Kwamishinar Ma’aikatar Gona ta Jihar Kaduna, Halima Lawal ta ce tana da yakinin daminar bana za ta yi albarka duk da barkewar cutar Kurona da matsalolin tsaro da ake fama da su a jihar. Ta yi wannan bayani ne a tattaunawar da aka yi da ita a Kaduna:

A halin da ake ciki na kulle, gwamnati ta lissafa wasu rukunin ma’aikata da sana’o’in da dokar zaman gidan ba ta shafe su ba saboda muhimmancinsu. Amama noma ba ya cikin wadannan ayyuka. Shin manona ba su a cikin masu ayyuka na musamman ne?

A gaskiya baa sanya manoma cikin masu ayyuka na musamman a sanarwar da aka fitar ba amma manoma suna ciki. Manoma suna cikin masu ayyuka na musamman, musamman a wannan lokaci na damina da kuma lokacin annoba irin wannan. Duk wadanda suke aiki a kowanne fanni na aikin gona ko samar da abinci wannan dokar ba ta shafe su ba kamar yadda dokar ta zo a hukumance. Duk wanda suke ayyukan da suka shafi samar da abinci a fannin noma wannan dokar ba ta shafe su saboda muhimancin ayyukansu ga al’umma.

Wadanne matakai Ma’akatar Gona ta dauka don manoma su samu damar yin noma a kakar bana musamman in aka yi la’akari da matsalolin tsaro da ake fama da su?

A gaskiya tun kafin damina ta fadi mun san babbar matsalarmu  ita ce matsalar tsaro saboda haka muka tuntubi abokan aikinmu da ke Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida kuma muka sanar da al’ummominmu da ke kananan hukumomi 23 cewa su sanya ido a kan harkar tsaro ta hanyar sanar da hukumar duk wadanda suke zargin ’yan ta’adda ne. Bugu da kari, muna aiki tare da Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi da shugabannin kananan hukumomin a matsayinsu na shugabannin al’umma kan gudummawar da za su bayar wurin kare rayuka da dukiyoyin al’ummarsu. Gwamnati ta dauki maganar tsaro da muhimmanci kuma harkar tsaro wani aiki ne na hadin gwiwa har da su kansu manoman. Saboda haka duk wasu matakan da suka kamata an dauka na ganin an samu damina mai albarka, abinci ya wadata musamman a wannan lokaci na annoba.

Jihar Kaduna cibiya ce ta noma, ita ce kan gaba a noman masara da tumatir kuma an ce cittar da ake nomawa a jihar ta fi ta ko’ina kyau a duniya. Wasu matakai kuka dauka don ganin cutar COBID-19 ba ta shafi wadannan amfanin gona ba?

Mun gode Allah duk da matsalolin da wannan annoba ta COBID-19 ta haifar a duniya, mu a Jihar Kaduna mun dauki matakai da wuri, don ganin wannan annoba ba ta shafi noma a fadin kananan hukumominmu 23 ba a bana ba. Saboda haka, Ma’aikatar Gona ta dukufa wurin ganin an yi amfani da duk wasu dabarun noma na zamani ta hanyar amfani da kimiyya da fasaha domin guje wa cakuduwar jama’a saboda a samu amfanin gona mai albarka kuma a dakile yaduwar wannan annoba ta Kurona. Mun fadakar da manomanmu ta kafafen yada labarai cewa su bi dokokin da gwamnati ta sanya da shawarwarin jami’an kiwon lafiya a yayin da suke gudanar da ayyukan nomansu. Alhamdulillahi duk alamu sun nuna za a samu wadattacen ruwan sama saboda haka muna da tabbacin daminar bana za ta yi albarka.

A baya kin ce kun dauki matakan ganin cewa kayan noma sun wadata. Yaya maganar farashin wadannan kayan noma?

Misali game da takin zamani, akwai tsarin samar da takin zamani na Gwamnatin Tarayya wanda take kawo takin NPK 20-10-10 a kan Naira dubu biyar da dari biyar. Maganar da ake ciki yanzu, gwamnati ta rage kudin wannan takin zuwa Naira dubu biyar a kowane buhu mai girman kilo hamsin. Saboda haka, muna kiran manoman Jihar Kaduna da sauran al’umma su sanya ido kan yadda ake sayar da takin kuma su kawo mana karar duk wanda aka kama da zargin sayar da takin a sama da Naira dubu biyar ko yana neman karkatar da takin. Domin kawo korafi ana iya tura mana sako ko kiranmu a wadannan lambobin waya: 08030453360 ko 08029133240. Bugu da kari, sauran kayan noma kamar iri da magungunan feshi, mun yi tsari da masu sayar da wadannan kayayyaki kan su sayar a kan kudi mai saukin farashi. Sannan za su kawo wadannan kayan noma zuwa kusa da manoma a kowace karamar hukuma saboda magance hadarin da ke cikin tafiye-tafiye zuwa wuri mai nisa domin sayo wadannan kaya.

Shin ina ne wuraren da manoma za su iya sayen wadannan kayan noma ba sai sun yi tafiya mai nisa ba?

Mun yi tsari mai kyau ta yadda duk masu sayar da iri da magungunan feshin nan za su kasance suna da rumfuna a kowace karamar hukuma a kusa da dakunan da ake sayar da taki a kananan hukumomi 23 da muke da su. Ta yadda in manomi ya saya taki, a gefe zai iya sayen iri ko maganin feshi da sauransu. Wannan shi ne tsarinmu a kowace karamar hukuma.

Wadanne matakai kuka dauka don ganin ba a samu faduwar farashin amfanin gona ba?

A hasashen da muka yi, ban jin za a samu faduwar fashin amfanin gona. Amma duk da haka wannan gwamnati ta kirkiri hukuma ta musamman mai suna, Kaduna Produce Management Company (KADPMC) wadda ke da alhakin aiki tare da manoma da kuma kamfanoni ko ’yan kasuwa don ganin an sayar da amfanin gona a farashi mai kyau. Wasu matakan sun hada da ba gwamnati shawara ta sayi amfanin gona ta ajiye a rumbunan ajiyarta in har ya zama babu kasuwa.

Shin ko akwai tunanin wannan annoba za ta shafi kokarin da gwamanti ke yi na ganin ta inganta noman citta a jihar don samun karin kudaden shiga?

Wannan annoba ta COBID-19 ba wani abu da ba ta shafa ba a duniya har da citta. Amma duk da haka manomanmu sun noma citta kuma suna kan nomawa. Ma’aikatarmu ta Aikin Gona tana nan tana aiki da kwararru da kuma abokan huldarmu don ganin yadda za a inganta noma da kasuwancin citta da sauran abubuwan amfanin gona.

Rashin farashi mai kyau a kasuwar duniya na daya daga cikin matsalolin da ke addabar manoman citta, wane kokari kuke yi don taimaka wa manomanta game da wannan matsala?

Mun tattauna da abokan huldarmu game da wannan matsalar. Duk da dai ba za mu iya magance matsalar dari bisa dari ba, amma mun yi kokari don ganin mun ilimantar da manomanmu cewa in suna da citta mai daraja za su samu farashi mai kyau. Sannan hukumarmu ta bunkasa aikin noma (Kaduna Agricultural Debelopment Agency – KADA), ta shirya wa manomanmu horarwa a lokuta daban-daban.

Bugu da kari, shirin nan bunkasa noma da inganta rayuwa na APPEALS na Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Bankin Duniya ma yana ba manomanmu horo kan yadda za a inganta noman citta. Sannan muna wayar da kan manomanmu kan muhimancin hadin gwiwa da kuma yadda za a samu kamfanoni masu sarrafa citta. Saboda haka wadannan suna cikin kokarin da muke yi na ganin mun bunkasa noman citta kuma mun kara darajarsa.

Wane mataki gwamnati za ta dauka don ganin ta kare manoma daga dillalai masu damfarar manoma su saye musu amfanin gona a kudi kalilan? 

Wannan wani abu mai sarkakiya amma gwamnatin nan na iya kokarinta wurin ganin cewa farashin amfanin gona ya yi daraja. Wasu matakan da muka dauka kamar yadda na yi bayani a baya shi ne ilimantar da manoman su san tsarin aikin noma, su san duk wasu masu ruwa-da-tsaki a harkar aikin wanda hakan zai dinke duk wata baraka a tsakaninsu da dillalai. Sannan muna wayar musu da kai kan muhimmacin kafa kungiyoyi wanda hakan zai kara musu karfi wurin bunkasa amfanin gona da kuma magance matsalolin da manoma ke samu a tsakaninsu da dillalai.