✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna Sane da Leah Sharibu —Gwamnatin Tarayya

Ministar Harakokin Mata ta ce gwamnati na fadi-tashin ganin an kubutar da Leah Sharibu da ragowar ’Yan Matan Chibok da ke hannun ’yan ta’adda

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kara kaimi don ganin an ceto Leah Sharibu, Dalibar Dapchi tilo da ta rage a hannun ISWAP bayan kungiyar ta saki abokan karatunta da ta sace su tare.

Minisatar Harkokin Mata, Pauline Tallen, ce ta bayyana hakan ga manema labarai a Abuja, in da ta ce duk da cewa ’yan ta’addan ba su sako Leah da ta shafe kimanin shekaru biyar a hannunsu ba, Gwamnatin Tarayya na ci gaba da tuntubar ’yan uwanta tare da ba su taimakon da ya dace domin kwantar musu da hankali.

“Ina tallafa musu ta kowace hanya da zan iya.

“Ina mai tabbatar muku cewa duk wata bukata da ta shafi dangin Leah da na kai gaban Shugaban Kasa ba ya wasa da ita.

“Har hotunan jirgi mai saukar ungulu da na tsaron da ya ba ni na je ga iyalin zan iya nuna muku.”

Ministar ta yi wannan batu ne a lokacin da take magana kan fadi-tashin da gwamnati ke yi don kubutar da Leah Sharibu da sauran Daliban Chibok da Boko Haram ta sace.

Ta ce, “Haka zalika duka da ahalin Sharibu ba a garin Chibok suke ba, da muka isa Chibok sai da muka shirya yadda za mu gana da su a sansanin sojojin saman Najeriya da ke Yola kuma mun tattauna da su kamar yadda Shugaban kasa ya umarta.”

Dahgane da sauran ’yan matan Chibok da ke cikin ’yan ta’addan kuwa, Dame Tallen, ta ce Gwamnatin Tarayyar ta damu matuka da halin da suke ji bayan ba su ji ba ba su gani ba, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kubuto da su.