✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna shirin dawo da sufurin keke ka’in da na’in a Najeriya —FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta ja hankalin ’yan Najeriya kan alfanun hawa keke musamman a bangaren lafiyar jiki.

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta ja hankalin ’yan Najeriya kan alfanun hawa keke musamman a bangaren lafiyar jiki.

Kwamandan hukumar na Jihar Kogi, Stephen Dawulung, ne ya yi jan hankalin, ta bakin Jami’in Ilimantarwar Hukumar, Ayodeji Oluwadunsin.

Sanarwa dai an fitar da ita ne a shirye-shiryen hukumar na gudanar da bikin zagayowar Ranar Keke ta Duniya ta 2022, da za a gudanar ranar 3 ga watan Yunin da muke ciki.

Taken bikin na bana dai shi ne ‘Hawa keke domin inganta muhalli da zamantakewa’.

Mista Stephen ya ce, “A tsawon shekarun da suka gabata, kasashen duniya da dama sun nuna yadda amfani da keke a matsayin hanyar sufuri yake da muhimmanci, da kuma inganta lafiyar jiki.

“Bayan kawata birane kamar yadda muke gani a kasashen Asiya da yake yi, amfani da abin hawan da ba ya fitar da hayaki, na dakile matsalar da iskar Carbon da mota da babur ke haifarwa ga iskar da muke shaka”, in ji shi.

Haka zalika ya ce yanzu haka hukumar tayi yarjejeniya da Kungiyar Hadin Kan Kasashen Duniya domin fara shirye-shirye, da ayyukan da za su dawo da amfani da Keke a Najeriya, a matsayin hanyar sufurin da za ta maye gurbin wadanda ake amfani da su a yanzu.

Ya ce dogaro motoci da babura, ya sanya ’yan Najeriya da ke rayuwa a birane ke fama da matsalar tashin farashin man fetur da dangoginsa, wanda hakan ke kara yawan man da kasar ke bukata, ga kuma cunkoson ababen hawa da ya ki karewa.

“A bangaren killace abin hawa kuma, Keke baya cinye kashi 10 na gurin da mota za ta ci, kuma kuma za ka iya ajiye shi ta kowacce fuska ba tare da wata matsala ba”, in ji shugaban hukumar ta FRSC.

“A bangaren lafiya kuma, yana hanawa da rage kiba, da lafiyar zuciya, da rage cututuukan damuwa, da na gabobi” in ji shi.

Don haka ya ce hukumar na fatan hadin guiwar da ta yi da kungiyar mahaya keke ta Jihar Kogi, da sauran masu ruwa da tsaki, na yin zagaye kan Kekunan zai inganta hanyar sufurin da kuma sauya tunanin al’umma a kai.

Sai dai Stephen ta bakin Ayodeji ya gargadi mahaya keken da su bi dokokin hanya kamar sauran masu abin hawa saboda lafiyar kowa.