✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna takaicin hargitsin da aka tayar a filin wasa na Abuja —NFF

Magoya bayan Super Eagles sun lakada wa wani likita duka kawo wuka wanda ya yi ajalinsa.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta bayyana takaicinta kan hargitsin da ya biyo bayan wasan neman tikitin zuwa gasar Cin Kofin Duniya da tawagar Super Eagles ta Najeriya ta yi da Black Stars ta Ghana ranar Talata.

Wasan wanda aka fafata a filin wasa na tunawa da Mashood Abiola da ke Abuja an tashi 1-1, lamarin da ya hana tawagar Super Eagles samun tikitin zuwa gasar kasancewa ita ce ta karbi bakunci.

Sakatare Janar na hukumar ta NFF, Muhammad Sanusi, ya shaida cewa suna bai wa ’yan Najeriya hakuri kan sakamakon wasan da ya ba kasar rashin cancantar shiga gasar Cin Kofin Duniya ta bana da za a yi a Qatar.

NFF ta kuma bayyana alhini kan mutuwar wani jami’in hukumar kwallon kafa ta CAF a yayin wasan.

Bayanai sun ce wani jami’in hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da kuma Hukumar CAF ta Afirka, Dokta Joseph Kabungo ya mutu ranar Talata a Abuja sakamakaon bugun zuciya bayan kammala karawa tsakanin Najeriya da Ghana.

Sai dai kuma wasu rahotanni na cewa, magoya bayan Super Eagles ne suka yi ajalin likitan a sakamakon lakada masa dukan kawo wuka, bayan tashi daga wasan wanda sakamakonsa ya fusata su.

Wani dan jaridar kasar Zambiya, Matimba Nkonje, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da mutuwar Kabungo a shafinsa na Twitter.