✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Munayah Yusuf Hassan: ’Yar Kano ta zama lauyar manyan kotunan Birtaniya

Munayah ta kammala karatunta a Jami’ar Bayero da ke Kano.

Wata ’yar Najeriya kuma ’yar asalin Jihar Kano, Munayah Yusuf Hassan, ta zama kwararriyar lauya ta manyan Kotunan Ingila da Wales.

An nada ta kwararriyar lauyar manyan kotunan Birtaniya a wani kwarkwaryan biki da aka yi ranar Juma’a a Landan, a cewar fitaccen lauyan nan mai kare hakkin dan Adam, Bulama Bukarti.

Munayah ta kammala karatunta a Jami’ar Bayero ta Kano, sannan ta kammala sanin makamar aiki a Makarantar Lauyoyi kafin komawarta Ingila da mijinta.

Kwararrun lauyoyin Manyan Kotunan Ingila da Wales suna aiki da bayar da shawarwari ga abokan huldarsu akan dokokin Ingila da Wales.

Haka kuma, suna aikace-aikace da dama na shari’a a fannin dokokin kasuwanci, iyali, laifukan al’umma da sauransu.