✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Munir: Arsenal ta dauki dan Najeriya mai shekara 9

Mahaifiyarsa da kakarsa sun halarci sanya hannu kan kwantaraginsa da kungiyar.

Munir Sada, mai shekara tara, dan asalin Zariya a Jihar Kaduna ya zama dan wasa a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kasar Birtaniya.

Dan Najeriyan shi ne zai goya riga mai lamba tara a rukunin kananan yara na kungiyar ta Arsenal.

Mahaifiyar Munir da kakarsa sun halarci sanyan hannu a kwantaragin daukar sa a kungiyar.

Dan wasan tare da mahaifiyarsa da kakarsa a loakcin da suka halarci sanya hannu kan kwantaragin zuwansa Arsenal.
Munir Sada yana taka leda a lokacin atisaye tare da abokan wasansa a Arsenal.
Munir mai shekara tara shi ne zai sanya riga mai lamba tara a kungiyar.
Sabon dan wasan na Arsenal a lokacin sanya hannu kan kwantaragin zuwansa kungiyar.
Munir Sada, dan asalin Zariya a Jihar Kaduna ya zama da wasan kungiyar Arsenal.
Sabon dan wasan na Arsenal a lokacin cike takardun komawarsa kungiyar.
Munir yana tsaka da wasa a lokacin wani atisaye a sabuar kungiyar tasa.
Ana tsaka da atisaye a Arsenal.