✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MURIC na neman gwamnati ta biya manoman da makiyaya suka yi wa ta’adi

MURIC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta biya manoma diyya wadanda Fulani makiyaya suka yi wa ta’adi a gonakinsu.

Kungiyar nan Mai Fafutukar Kare Hakkin Musulmai ta Najeriya (MURIC) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta biya manoma diyya wadanda Fulani makiyaya suka yi wa ta’adi a gonakinsu.

Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayayana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

A cewar kungiyar, akwai tarin hujjoji na bidiyo dake nuna yadda makiyayan suka yi wa gonakin manoman ta’adi.

Ya ce, “MURIC yanzu haka ta tura wakilanta jihohi domin tattara bayanai kan irin barnar da makiyaya suka yi a gonakin manoma.

“Mun neme su da su tattaro bayanai daga dukkan jihohin har da Babban Birnin Tarayya Abuja.

“A zahirin gaskiya kuma mun gamsu da irin bayanan da suke ba mu,’’ inji Daraktan na MURIC.

Farfesa Ishaq ya kuma yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su dauki nauyin biyan diyyar, yana mai cewa bayyane yake a zahiri cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta fara biyan manoman diyyar asarar da suka yi ba.

“Saboda haka muna sake jaddada kiranmu ga gwamnati kan ta bullo da sabbin hanyoyin biyan diyya, muna da hujjoji da bayanai na irin barnar da aka yi.

“Hakan ne kadai zai tabbatar da wanzuwar adalci da daidaito,’’ inji shi.