✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

MURIC ta bukaci a hukunta Rabaran saboda kaiwa Musulman Nsukka hari

MURIC ta yi kira da a gaggauta kamawa tare da gurfanar da Rabaran Fada Godfrey Igwebuike

Kungiyar nan mai rajin kare hakkokin Musulmai a Najeriya ta MURIC ta yi kira da a gaggauta kamawa tare da gurfanar da Rabaran Fada Godfrey Igwebuike Onah.

Kungiyar dai ta yi kiran ne saboda zargin da take masa na hannu a rikicin da ya kai ga kona masallatai a garin Nsukka na jihar Enugu a kwanan nan.

MURIC ta zarge shi da yin amfani huduba a cocinsa wajen tunzura mabiya addinin Kirista su kai wa Musulmin yankin hari tare da lalata musu masallatai.

Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola wanda ya yi kiran cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Juma’a ya ce kungiyar tasu na goyon bayan matsayin Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya wajen kiran Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta kama shi.

Sanarwar ta ce, “MURIC na da shaidar bidiyon da Rabaran Fada Onah yake tunzura mabiyansa ‘yan kwanakin da suka gabata.

“Munji inda yake cewa ba za ta sabu ba a garin Nsukka su kyale Musulmai su rika kiran sallah da karfe 4:00 na Asuba.

“Babu ko tantama wannan yunkuri ne a fakaice na kira da a kai hari tare da lalata masallatai a Nsukka da ma yankin Kudu Maso Gabas baki daya,” inji shi.

MURIC ta kuma ce an kona akalla masallatai biyu a wannan yankin cikin mako daya da yin wannan hudubar, wacce ta ce an yi ta ne da nufin jefa kiyayya tsakanin mabiya addinan biyu.

MURIC ta ce ta hanyar hukunta Fadan ne kawai za a yi wa tufkar hanci kuma ya zama izina ga wasu.