✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Murnar cika shekara 29: Yadda jihohi 12 na Najeriya suka samo asali

A jiya Alhamis, 27 ga watan Agustan 2020, wasu jihohi 12 daga cikin 36 na Najeriya suka cika shekara 29 da ta kafuwa. Jihohin da…

A jiya Alhamis, 27 ga watan Agustan 2020, wasu jihohi 12 daga cikin 36 na Najeriya suka cika shekara 29 da ta kafuwa.

Jihohin da aka kirkiro shekaru 29 da suka gabata sun hadar da; Abia; Adamawa; Anambra; Delta; Edo; Enugu; Jigawa; Kebbi; Kogi; Osun; Taraba da kuma Yobe.

An kirkiri jihohin ne a ranar 27 ga watan Agusta na 1999 a lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wanda ya kasance mutum na takwas a cikin jerin wadanda suka jagoranci kasar.

Wasu daga cikin jihohin an tsakuro su ne daga wasu jihohi yayin da wasunsu suka fito daga wata jihar da aka rabe ta gida biyu.

Ga dai yadda jihohin suka samo asali kamar yadda kundin tarihi ya tabbatar;

Abiya – Daga Jihar Imo.

Adamawa – Daga tsohuwar jihar Gongola, wadda aka gididdiba ta gida biyu ta zama Adamawa da Taraba.

Anambra – Daga tsohuwar Jihar Anambra.

Delta – Daga tsohuwar Jihar Bendel; wadda aka raba ta zamto Delta da Edo.

Edo – Daga tsohuwar Jihar Bendel; wadda aka raba ta zamto Edo da Delta.

Jigawa – Daga Jihar Kano.

Kebbi – Daga Jihar Sakkwato.

Kogi – Daga wani yanki na jihohin Kwara da Binuwai.

Osun – Daga Jihar Oyo.

Taraba – Daga tsohuwar jihar Gongola, wadda aka gididdiba ta gida biyu ta zama Taraba da Adamawa.

Yobe – Daga Jihar Borno.