✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musa Hasahya: Mutumin Uganda mai mata 12 da ’ya’ya 102 da jikoki 578

Mutumin ba ya iya tuna sunayen wasu daga cikin matansa.

Wani mazaunin yankin karkarar kasar Uganda Musa Hasahya Kasera, ya ce ya gaji da haihuwa haka, saboda haka a kai kasuwa, bayan ya haifi yara 102 tare da matansa guda 12, abinda ya kai shi samun jikoki 578.

Hasahya da ke kauyen Bugisa a Yankin Butaleja ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewar ganin yadda halin lafiyarsa ke tabarbarewa da kuma eka 2 kacal na filin noman da ya mallaka, ya zama dole ya sake nazarí a kan rayuwarsa, musamman ganin biyu daga cikin matansa sun gudu.

Mutumin mai shekaru 68 da yanzu haka ba shi da wani aikin yi, ya mayar da kauyensu wajen yawon bude ido ga baki wadanda ke tattaki domin gani da idonsu shin wannan lamari haka yake da gaske, yayin da sauran matansa ke shan maganin hana daukar ciki.

Hasahya ya ce babu tantama matansa na shan maganin hana daukar ciki amma shi baya sha, duk da yake baya fatar samun karin haihuwa saboda ya fahimci kuskuren da ya yi wajen haifan yaran da ba zai iya daukar nauyinsu ba.

Shi dai wannan magidanci ya yi aurensa na farko ne a shekarar 1972 lokacin wani bikin gargajiya, yayin da yake da shekaru 17 da haihuwa a duniya, abinda ya kai shi samun ’yarsa ta farko Sandra Nabwire shekara guda bayan auren.

Saboda su biyu kadai mahaifiyarsu ta haifa, ya sa wansa da danginsa suka bukace shi da ya kara auro wasu mata domin samun yara da yawa da za su fadada danginsu.

Hasahya ya ce wannan ta sa ya gamsu da shawarar da aka ba shi a matsayinsa na dillalin shanu kuma mahauci inda ya dinga kara mata har wadanda suke kasa da shekaru 18.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya ce yaran Hasahya 102 na tsakanin shekaru 10 ne zuwa 50, yayin da matarsa mafi karancin shekaru ke da shekaru 35 a duniya.

Hasahya ya ce baya iya tuna sunayen da yawa daga cikin yaran nasa in banda babbansu da dan autansu, abin da ya sa uwayensu mata ke tuna masa sunayensu.

Wani abin takaici shi ne wannan mutumin ba ya iya tuna sunayen wasu daga cikin matansa har sai ya tuntubi daya daga cikin ’ya’yansa Shaban Magino mai shekaru 30 wanda ke aikin koyarwa a makarantar firamare, yake kuma taimakawa wajen tafiyar da al’amuran gidansu a matsayinsa na daya daga cikin yaran gidan da suka samu ilimi.

Domin warware rikice rikicen da suka taso a tsakanin iyalan gidan, Hasahya ya ce su kan gudanar da taron wata-wata a tsakaninsu.

Wani jami’in karamar hukumar yankin da ke kula da Bugisa, kauyen da ke dauke da mutane kusan 4,000 ya ce duk da matsalolin da ake fuskanta, Hasahya na bai wa ’ya’yansa tarbiya ta gari, kuma babu matsalar sata ko kuma fada a tsakaninsu.

A shekarar 1995 ce aka haramta auren yara – wadanda ba su kai shekaru 18 ba – yayin da aka halasta auren fiye da mace guda a bisa tsarin al’adu a kasar da ke Gabashin Afirka.