✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar AlKur’ani: Ganduje ya ba gwaraza kyautar Naira miliyan 5

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da kyautar naira miliyan biyar ga gwarazan da suka yi nasara a musabakar AlKur’ani ta kasa karo na 35 da…

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da kyautar naira miliyan biyar ga gwarazan da suka yi nasara a musabakar AlKur’ani ta kasa karo na 35 da aka kammala ranar Asabar a birnin Dabo.

Wata sanarwa da sakataren yada labarai na mataimakin Gwamnan Kano Hassan Fagge ya fitar, ta ce kowane daya daga cikin gwarazan biyu zai samu kyautar kudi ta naira milyan 2.5.

Gwarzon wannan shekara a rukunin maza, shi ne Muhammadu Auwal Gusau daga Jihar Zamfara, wanda ya doke sauran abokan karawarsa a rukunin haddar Izifi sittin da Tajwidi da kuma Tafsirin AlKur’ani.

A rukunin mata kuma, wata ’yar jihar Kano ce ta zama gwarzuwar a musabakar ta bana mai suna Nusaiba Shu’aibu Ahmad.

Akalla mahaddatan AlKur’ani fiye da 300 ne suka fafata a musabakar wacce aka shafe fiye da mako daya ana gudanarwa a harabar filin taro na Jami’ar Bayero da ke Kano.

A jawabinsa yayin rufe taron, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce maza 180 da kuma mata 190 ne daga dukkan jihohin kasar ciki har da Abuja suka fafata a gasar haddar AlKur’ani ta tsawon kwanaki tara.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, ya yaba da yadda mahaddatan suka fafata a bangarori shida na musabar tun daga kan Izifi biyu zuwa Izifi sittin tare da Tajwidi da kuma Tafsiri.

“A yanzu za mu bayar da kyautar naira miliyan 2.5 ga kowane daya daga cikin gwarazan na rukunin maza da mata, kuma gwamnatinmu ta sanya hakan a matsayin wani tubali na inganta ayyukanta a bangaren ilimin Addinin Islama musamman abin da ya shafi karatun AlKur’ani da haddar shi.”

“Wannan shi ne dalilin ya muka kafa Hukumar Kula da Makarantun AlKur’ani da Islamiya a Jihar Kano, wanda har kawo yanzu take ci gaba da samun nasarori masu yawa wajen bunkasa ilimin addinin Musulunci,” in ji Gawuna.