✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mustafa Shehu: Mutumin Kano da ya zama Shugaban Kungiyar Injiniyoyi ta Duniya

Injiniya Mustafa Shehu wanda dan asalin Jihar Kano ne, shi ne bakar fata kuma mutumin yankin Sahara na farko da zai jagoranci WFEO.

A ranar Larabar makon jiya ce Injiniya Mustafa Balarabe Shehu ya zama sabon zababben shugaban kungiyar Injiniyoyi ta Duniya da ake kira WFEO (World Federation of Engineers Organization).

Rahotanni sun tabbatar da cewa Shehu ne ya lashe zaben wanda Kungiyar Injiniyoyi da masu zayyana na reshen kasar Kosta Rika su ka gudanar wato Colegio Federado de Ingenieros y de Arquitectos de Costa Rica.

Injiniya Mustafa Shehu wanda dan asalin Jihar Kano ne, shi ne bakar fata kuma mutumin da ya fito daga yankin Sahara na farko da zai jagoranci  kungiyar ta WFEO.

Wannan ne karon farko da aka samu wani mutumin Sahara daga nahiyar Afrika da ya dare kan wannan kujera tun bayan kafuwar kungiyar shekaru 54 da suka gabata.

Kamar yadda WFEO ta bayyana a shafinta na Twitter, Mustafa Balarabe Shehu FNSE FAEng ya lashe zaben shugabancin WFEO da aka yi a makon nan.

Sanarwar da WFEO ta fitar a ranar Alhamis, 10 ga watan Maris 2022, ta tabbatar da nasarar Injiniya Shehu da cewa, “Muna taya Engr Mustafa B. Shehu dan Najeriya murna, wanda ya zama zababben shugaban kungiyar WFEO a taron da aka yi a San Jose, Costa Rica.

Injinya Mustafa Balarabe Shehu da iyalinsa da sauran abokan aiki.

Bayanai sun ce WFEO ce babbar kungiyar Injiniyiyo ta Duniya mai zaman kanta.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Injiniya Shehu ya mika godiya ta musamman ga ’yan uwa da abokan arziki da suka taimaka masa da addu’o’i da goyon baya har ya cim ma wannan nasara.

Injiniya Shehu ya shugabanci Kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya NSE reshen Kano daga 2000 zuwa 2022 da mataki na kasa daga shekarar 2012 zuwa 2013 da kungiyar Injiniyoyin Afrika daga 2015 zuwa 2016. Kafin yanzu ya yake rike kujerar Mataimakin Shugaban WFEO.

Shehu ya yi aiki a wurare da-dama kafin ya bude kamfani na kansa, Amal Engineering Services wanda ya sauya sunansa zuwa Mustafa Balarabe Shehu Engineering Limited.

An haifi sabon zababben shugaban na WFEO a ranar 12 ga watan Afrilun 1963. Mujallar Abusites ta ce mahaifin Injiniyan watau Alhaji Shehu Salihu ya rasu ne a lokacin yana karamin yaro tun bai wuce shekaru 12 a duniya ba.

Sai dai mutuwar mahaifinsa ba ta hana shi ya ci gaba da gwagwarma a rayuwa ba, inda ya rika fadi-tashin da ya kai ga ya samu damar yin karatu har zuwa matakin zama injiniyan lantarki a Jami’ar ABU Zaria a 1985.

Ya soma karatun Firamare a Jahun a Jigawa, sannan ya tafi Sumaila kafin daga bisani ya koma Firamaren Kwalli da ke kwarywar birnin Kano inda a nan ya karkare.