✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulma ta zama Magajin Gari mace ta farko a yankin Amurka

Ita ce ’yar asalin Somaliya kuma bakar fata ta farko da aka zaba magajin gari a kasar Amurka

Wata Musulma ’yar gudun hijira ta zama mace ta fakro bakar fata da ta zama Magajin Garin Mainea wanda kashi 90 cikin 100 na mazaunansa fararen fata ne a kasar Amurka. 

Deqa Dhalac, mai shekara 53, wadda ’yar gudun hijira ce daga kasar Somaliya ta zama Musulma bakar fata ta farko a matsayin Magajin Garin da ke yankin South Portland ne bayan shugabannin yankin — wadanda dukkansu fararen fata ne — sun zabe ta ba tare da hamayya ba.

Sudan: An kashe mutum 138 a sabon rikicin kabilanci a Darfur

’Yan Arewa sun shirya wa Buhari gagarumar zanga-zanga

Da take jawabi bayan karbar rantsuwar kama aiki, Dhalac ta ce: “Mutane na da irin ra’ayoyinsu… amma a yau da gobe za su zo su san ko kai wane ne, su saurare ke har su saimaka maka.”

A shekarar 1992 ne Deqa Dhalac ta koma kasar Amurka da zama a matsayin ’yar gudun hijira bayan yakin basasa ya barke a kasar Somaliya. Ita ce kuma mutum na farko daga Somaliya da ya zama magajin gari a fadin kasar Amurka.

Deqa Dhalac ta bayyana cewa ta shiga siyasa ne saboda kawar muguwar siyasar kyamar Musulunci irin ta tsohon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump.

Ta ce a lokacin da ta fara takara a 20218 wasu mutane tsoro suke ji su bude mata kofa ta shiga gidajensu a yayin da take bi gida-gida domin yakin neman zabe; Wasu ba su ma yi zaton tana iya yin magana da harshen turancin Ingilishi ba.

Don haka ta ce tana alfahari da nasarar da ta samu kuma tana fata zai zama kyakkyawan misali abin koyi ga sauran al’ummomi marasa rinjaye da masu tasowa a kasar.

Bayan zaben ta a yankin da Kudu da gabar Maine a ranar Talata, kungiyar shugabannin yankin ta ce, “A matsayinta na bakar fata kuma Musulma ta farko a majaliasr shugabannin Portlan, Magajiyar Gari Dhalac babbar jigo ce wajen kawo canji a cikin wannan al’umm.