✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Musulmi su hada kai don zaben shugabanci nagari —Gumi

Gumi ya bukaci Musulmi da suke sanya dukiyarsu don gina dakin Allah.

Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya ja hankalin Musulmi da su hada kansu don zaben shugabanci nagari a Zaben 2023 da ke tafe. 

Malamin ya bayyana haka ne a jawabinsa yayin kaddamar da aikin ginin Masallacin Dan Fodio a Jihar Kaduna.

“Dole ne mu zabi shugaba na gari, mu zabi shugaba mai tsoron Allah, kuma shugaba mai mutunta addininmu, idan muka yi haka to sauran sai mu bar wa Allah,” in ji shi.

A cewarsa, hadin kan musulmi umarni ne daga Allah idan har suna son su yi karfi a tsakaninsu.

Gumi ya kuma jaddada bukatar al’umma su bayar da tasu gudunmawar wajen sake gina masallacin, inda ya ce fadada masallaci sunna ce ta Annabi (S.A.W)

A nasa jawabin, Sarkin Zazzau Ambassada Ahmad Nuhu wanda Khadi Muhammad Inuwa Aminu (Waziri) ya wakilta, ya bukaci al’ummar Musulmi da su bayar da gudunmawa mai yawa don sake gina masallacin.

A cewarsa, yin hakan zai sa mutum ya samu lada mai yawa daga Mahalicci.

Kazalika, Shugaban taron, Birgediya Janar Abdulkadir Abubakar Gumi (mai ritaya), ya bayyana cewa masallacin Dan Fodio shi ne wuri na biyu mafi muhimmanci ga kungiyar Izala bayan gidan mahaifinsa Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi.

Ya kuma yi tsokaci kan hadin kan musulmi wanda ya bayyana cewa yana da matukar muhimmanci ga wanzuwar al’umma, inda ya bayar da tabbacin kammala aikin masallacin kamar yadda aka tsara nan ba da dadewa ba.