✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulunci ya bai wa mata damar samun ilimi da aiki —Taliban

Gwamnatin Taliban ta ce tana kokarin samar da ‘yanayi mai aminci’ ga ’yan mata a makarantu da wuraren aiki a kasar Afghaninstan

Gwamnatin Taliban ta ce tana kokarin samar da abin da ake kira ‘yanayi mai aminci’ ga ’yan mata a makarantu da wuraren aiki a kasar Afghaninstan.

Ma’aikatar Ayyukan Jin Kai na Taliban, ta jaddada cewa, addinin Musulunci ya bai wa mata ’yancin neman ilimi da yin aiki da sana’o’i, don haka gwamnatin ke kokarin samar wa mata da ’yan mata a kasar yanayi mai aminci a makarantun sakandare da wuraren aiki.

“Dole ne in ce Musulunci ya bai wa mata ’yancin neman ilimi da ’yancin yin aiki da kuma yin kasuwanci.

“Tun da Musulunci ya yarda da hakan, to wane ne ni zan hana,” in ji kakakin Ma’aikatar, Sadeq Akif Muhajir, ha hirarsa da kafar yada labarai ta Al Jazeera.

Ya yi wannan bayani ne shekara guda bayan da kungiyar ta karbe mulkin kasar Afghanistan tare da sanya takunkumi a kan wasu abubuwa da dama da ake gani a matsain take hakkokin mata, ciki har da haramta mutu karatun sakandare.

Matakan da kungiyar ta dauka dai ya janyo suka daga kasashen duniya da kuma kakaba wa gwamnatin takunkumi.

Bayan hawar kungiyar ta Taliban kan karagar mulki, ta dauki wasu matakai da suka hada da rufe makarantun sakandaren ’yan mata a fadin kasar.

Ta kuma wajabta wa mata sanya hijabi da nikabi a wuraren aiki da a bainar jama’a, sannan ta haramta musu yin tafiya mai nisa ba tare da wani namiji muharraminsu ba.

Kasashen duniya dai na ganin haramcin tafiye-tafiyen mata ba tare da muharrami da kungiyar ta sanya ba ya yi daidai da salon mulkin Taliban a cikin shekarun 1990.

A wancan lokacin kungiyar ta hana ’yan mata da mata zuwa makarantu ko fitowa su gudanar da harkokinsu a bainar jama’a.