✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutane 11 sun mutu a yunkurin juyin mulkin Guinea Bissau

An so a kifar da gwamnatin Shugaba Umaro Sissoco Embalo.

Gwamnatin Guinea Bissau ta ce a halin yanzu mutum 11 ne aka tabbatar da mutuwarsu a yunkurin juyin mulkin da aka yi a ranar Talata inda aka so a kifar da gwamnatin Shugaba Umaro Sissoco Embalo.

Sojoji da farar hula na daga cikin wadanda suka rasu. An kaddamar da wani babban bincike domin gano ’yan bindigar da suka yi wannan aika-aika.

Sojojin kasar dai na ci gaba da shawagi kan titunan babban birnin, inda aka soma bude shaguna da bankuna sai dai akwai kwastamomi kadan a kasuwannin da ke Bissau.

Har yanzu wurin da aka yi bata-kashin wanda ke makwaftaka da gidan gwamnatin kasar a rufe yake.

Guinea Bissau dai ta yi kaurin suna wajen safarar hodar ibilis tsakanin yankin Latin Amurka da Turai wanda hakan ya sa aka soma tunanin gungun masu safarar kwayoyi ne suka yi wannan aika-aika