✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutane da dama sun mutu bayan fashewar tankin iskar gas a Legas

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 9:00 na safiyar ranar Talata.

Mutane da dama aka tabbatar da rasuwarsu bayan fashewar wani tankin iskar gas a yankin Ladipo da ke unguwar Mushin a Jihar Legas.

Kazalika, wasu da dama kuma sun samu raunuka daban-daban sakamakon fashewar.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 9:00 na safiyar ranar Talata.

Ibrahim Farinloye, jami’in Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ya shaida wa wakilin Aminiya cewa tankin da ya fashe mallakin kamfanin LPG ne da ke kan titin Ojekunke a unguwar sayar da safayar kayayyaki ta Ladipo.

A cewarsa, “Ya zuwa yanzu, an gano gawarwakin mutum uku, maza biyu da mace daya, yayin da aka ceto wani jariri da ransa, kuma an kai shi asibiti.

“Yanzu haka muna ci gaba da aikin ceton mutane.

“Ma’ikatan Sashen Kiyaye Annoba na ’Yan Sanda da ma’aikatan kwana-kwana na NEMA da LASEMA na ci gaba da aikin ceton,” inji shi.