✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutane su tashi su kare kansu daga ’yan ta’adda — Sheikh Jingir

Ya ce bai kamata ’yan tsirarun mutane su rika tashin garuruwa ba

Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga al’umma su rika tashi tsaye don kare kansu da garuruwansu daga hare-haren ta’addanci.

Malamin ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya, a garin Jos.

Ya ce bai kamata ba a ce ’yan ta’adda mutum 20 su zo garin mutum 1,000, su kama mutane su tafi da su ba tare da samun turjiyar mutanen garin ba.

Ya ce ya kamata mutane su hada kai, su tashi kare garuruwansu, su zakulo munafukan da ke cikinsu.

Ya bayyana cewa wasu bata-gari kuma makiya ci gaban kasa a ciki da waje suna ta bata sunan Najeriya, kan rashin zaman lafiya a kafofin yada labarai na yanar gizo.

“Yau din nan sama da kasuwanni dubu sun ci a Najeriya. Kuma a yau din nan dubban manoma sun je gonakinsu, sun yi aiki sun koma gida lafiya.

“Amma idan ka dubi abubuwan da suke yadawa a kafofin yada labarai na yanar gizo sai ka dauka babu wanda ya isa ya fito a Najeriya. Kullum suna yada labaran firgita al’ummar kasar nan. Ya kamata masu kishin kasar nan su fito su rika yin magana, kan wadannan abubuwa da suke faruwa.”

Sheikh Jingir ya kuma nuna takaicinsa kan faduwar darajar Naira.

“Ni din nan ina harkokin kasuwanci a shekarar 1980, a lokacin na san Dala ba ta kai darajar Naira ba. Ya kamata gwamnati ta tuhumi Gwamnan Babban Bankin Najeriya kan karyewar darajar Naira.”

Sheikh ya ce akwai lalatattu a cikin gwamnatin nan da suke yi mata makarkashiya.

Don haka ya yi kira ga Shugaban Qasa ya kafa mutanen da zai rika jin halin da talakawan kasar nan suke ciki.