✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen ake zargi da kashe Kwamishina a Katsina sun shiga hannu

’Yan sanda sun kama wasu mutane kan zargin su da hannu a kisan Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Jihar Katsina, Dokta Rabe Nasir

Rundunar ’Yan Sanda Jihar Katsina ta ce ta kama wasu mutane da take zargi da hannu a kisan Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Jihar Katsina, Dokta Rabe Nasir da aka yi ranar Alhamis.

Labarin mutuwar kwamishinan ya bayyana ne a maracen ranar a Rukunin Gidajen Fatima Shema da ke garin Katsina.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Sanusi Buba, ya ce sun fara kama wasu da suke zargi da hannu a kan mutuwar Kwamishinan wanda a halin yanzu gawarsa ke ma’ajiyar gawa da ke Babbar Asibitin Katsina.

Sanusi Buba ya ce jami’ansa sun dukufa wajen binciko wadanda suka yi wannan aika-aika.

Jihar Katsina dai na daga cikin jihohin da suke fuskantar hare-haren ’yan bindiga ta hanyoyi iri dabam-daban.

Ana sa ran za a yi jana’izar mamacin a ranar Juma’a a Masallacin Juma’a na GRA a garin Katsina.