✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mutanen da ke fuskantar barazanar yunwa a duniya sun kai miliyan 45’

Hukumar ta ce ana bukatar Dalar Amurka miliyan bakwai don dakile barazanar.

Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da ke fuskantar barazanar karancin abinci a kasashe 43 na duniya a bana sun kai miliyan 45.

Ana dai ta’allaka tashin da adadin ya yi daga miliyan 42 a farkon wannan shekarar zuwa miliyan 45 da rikicin kasar Afghanistan.

Hakan, a cewar shirin kula da abinci na majalisar, WFP a ranar Litinin, ya biyo bayan samun karin mutum miliyan ukun da ke fuskantar barazanar a kasar.

Shugaban WFP, David Beasly ya ce, “Miliyoyin mutane ne ke cikin barazana. Mun fuskanci kalubale sakamakon annobar COVID-19 wacce ta kara ta’azzara matsalar yunwa.

“Alkaluman kwana-kwanan nan sun  nuna cewa akalla akwai mutum miliyan 45 da ke cikin wannan barazanar.

“Farashin man fetur, kayan abinci da takin zamani duk sun yi tashin gwauron zabo, hakan kuma na haifar da babbar barazana a kasashen Afghanistan da Yemen da kuma Syria,” inji shi.

Hukumar ta kuma ce ana bukatar Dalar Amurka miliyan bakwai matukar ana son magance barazanar.

“Matsalar yunwa ta fara jefa iyalai a wasu kasashen cikin tsaka mai wuya; wasu na aurar da ’ya’yansu da wuri, wasu na cire su daga makaranta, wasu kuma sun koma cin fara da sauran kwari.

“Akwai ma rahotannin da suke cewa a kasar Afghanistan, wasu iyayen sun fara sayar da ’ya’yansu, duk a kokarin nema wa kansu mafita,” inji Shugaban na WFP.

Ana dai fuskantar rahotannin karuwar yunwa a kasashen Habasha da Haiti da Somalia da Angola da Kenya da kuma Burundi, kamar yadda hukumar ta tabbatar.