Mutanen da suka bi barawo cikin rafi sun bace | Aminiya

Mutanen da suka bi barawo cikin rafi sun bace

Ruwa
Ruwa
    Abubakar Muhammad Usman da Mumini AbdulKareem, Ilorin

Wasu mutum biyu da suka bi wani barawo da ya tsere cikin rafi a yankin sun shafe kwanaki uku ba tare da an gan su ba.

Wani ganau ya bayyana wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 12 na rana a yankin Amilengbe na Jihar Kwara, bayan sun bi barawon cikin rafi a yayin da ya ke kokarin tserewa.

“Ihun da ake na barawo, barawo ne ya jawo hankalin mutanen da suke kusa da rafin.

“Ba a yi aune ba barawon ya yi tsalle ya fada cikin rafin, su ma mutum biyun suka fada suka bi shi.

“Bayan minti 30 shiru ba mu gan su ba, nan take muka sanar da Hukumar Kashe Gobara don kawo musu dauki,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu.

Da muka tuntubi shugaban sashen yada labarai na hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara, Hassan Adekunle ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, “Mun fahimci cewa barawon bayan ya yi wa wasu ’yan kasuwa ’yan kabilar Igbo da ke kusa da yankin Aminlengbe sai ya fada rafi. Amma har yanzu ba mu gano ko daya daga cikin wadanda suka fada ruwan ba, ko a raye ko a mace,” kamar yadda ya bayyana.