✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen da suka mutu a rushewar gini sun kai 8

Ya zuwa tsakar daren ranar Lahadi, masu aikin ceto a ginin da ya rushe a Jihar Legas sun kara samo gawar wata mata daga cikin…

Ya zuwa tsakar daren ranar Lahadi, masu aikin ceto a ginin da ya rushe a Jihar Legas sun kara samo gawar wata mata daga cikin baraguzan ginin, wanda hakan ya kai adadin wadanda suka mutu a ciki zuwa takwas.

Maza shida da mata biyu ne dai aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu da dama kuma suka sami munanan raunuka a ginin da ya rushe a kan titin Odo da ke Karamar Hukumar Eti-Osa.

An dai hako gawar matar ne da misalin karfe 11:52 na dare kuma masu aikin ceton na ci gaba aiki.

Yanzu haka wasu mutum goma da suka sami kananan raunuka wadanda aka tono daga cikin karikitai na asibitoci suna samun kulawar gaggawa.

Kangon ginin benen mai hawa uku ya rushe ne da yammacin ranar Lahadi.

Binciken Hukumar Agaji ta jihar Legas (LASEMA) ya gano cewa tun da farko sai da Hukumar Kula da Gine-gine ta Jihar Legas (LASBCA) ta bayar da umarnin dakatar da ginin saboda karya ka’ida.

Ko a kwanan na sai da aka zargi mai gidan da dora wani sabon gini a kai sa’o’i kadan kafin rugujewar ginin da ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Jihar Legas ta jima tana fama da matsalar rushewar gine-gine sakamakon rashin yin masu inganci wanda hakan yake jawo asarar dimbin yawa.