✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen gari sun babbake ‘barawon babur’ a Bauchi

Fusatattun mutanen garin sun kone shi da ransa

Wasu mutane sun kone wani mutum mai matsakaicin shekaru da ake zargin barawon babur ne a kauyen Chinade da ke Karamar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi.

An kona mutumin ne wanda ba a kai ga sanin sunansa ba kan zargin satar babur ranar Lahadi a garin Hardawa da ke Karamar Hukumar Misau da ke Jihar.

Mutanen garin na Chinade sun ce an biyo mutumin ne tun daga Hardawa har zuwa garin nasu, kuma matasa sun lakada mass duka ne kafin daga bisani suka banka masa wuta.

Har ila yau, sun shaida wa wakilinmu cewa mutumin da ake zargin ya saci babur ne a kasuwar Hardawa kuma ya gudu kafin a bi shi zuwa Chinade wanda ba shi da nisa daga Hardawan, amma a wata Karamar Hukumar ta daban.

Rahotanni sun ce lokacin da aka gano shi a Chinade, sai aka ankarar da matasa, lamarin da ya jawo hankalin jama’a wadanda suka kama shi suka yi masa dukan tsiya.

Sai dai duk da haka, mutanen garin ba su gamsu da dukan da aka yi masa ba, sai jama’a suka banka masa wuta, suna kallonsa ya kone kurmus.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Umar Mamman Sanda, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan abin da ya bayyana a matsayin ta’addanci da rashin imanin da aka aikata.

Sanda ya ce maimakon su kai wanda ake zargin gaban ’yan sanda domin gudanar da bincike da kuma gurfanar da shi gaban kotu, sai suka yi wa wanda ake zargin hukuncin kisan gilla, ba tare da bin doka ba.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Ahmed Mohammed Wakili ya fitar, ya ce Kwamishinan ya bayyana wannan aika-aika a matsayin “abin kunya da kuma saba wa dokar kasarmu mai daraja.”

Kwamishinan ya gargadi al’ummar Jihar da cewa rundunar sa ba za ta bari wasu marasa kishin kasa a cikin al’umma su ci gaba da daukar doka a hannunsu ta hanyar kashe wadanda ake zargi da aikata laifukan da suka saba wa doka ba.

Ya ce babu wanda ke da hurumin yi wa wanda ake tuhuma hukunci sai kotu