✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen gari sun kama masu garkuwa da mutane a Katsina

Jama’ar gari sun yi wa masu garkuwa da mutane kofar rago suka kuma cafke su a lokacin da suka yi kokarin sace wata mata. Masu…

Jama’ar gari sun yi wa masu garkuwa da mutane kofar rago suka kuma cafke su a lokacin da suka yi kokarin sace wata mata.

Masu garkwar sun samu tirjiya ne daga ’yan banga a kauyen Yauni na Karamar Hukumar Safana ta Jihar Katsina, inda suka yi kokarin dauke matar.

Sanarwar hakan da rundunar soji ta Operation Sahel Sanity ta fitar ta ce “Wanda ake zargin sun je sace wata mata ne amma ’yan banga suka yi masa tirjiya.

“Abokinsa ya tsere kafin isowar sojoji, amma ya tabbatar da cewa shi yaron wani shugaban masu satar mutane da ke zaune a Dajin Tsafe ne mai suna suna Mallam Ya’u. Muna bin sawun abonkan nasa domin kamo ’yan gungun”, inji rundunar.

Mukaddashin Darektan Yada Labarai na Rundunar Taro, Birgediya Benard Onyeuko, ya ce, “Sojoji sun kubutar da wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su, suka kuma cafke mutum daya daga cikin masu garkuwar, yayin da saura suka tsare a garin Daudawa Daudawa na Karamar Hukumar Faskari”.