✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen gari sun kona ‘barawon babur’ a Kano

Bayan lakada masa duka ya kwanta magashiyyan sai kuma suka cinna masa wuta.

Fusatattun mutanen gari sun cinna wa wani da ake zargi da satar babur wuta a Karamar Hukumar Wudil ta Jihar Kano.

Dubun mutumin ta cika ne bayan ya dauki wani babur a Wudil, kafin ya tafi da shi jama’a suka hango shi suka yi masa ihu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce bayan mutanen gari sun bi wanda ake zargin a guje ne suka yi kicibus da shi a kauyen Garin Da’u a tsallaken Gadar Wudil, inda suka lakada masa dukar kawo wuka.

Kakakin Runduar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce bayan mutanen sun yi wa wanda ake zargin duka ya kwanta magashiyyan sai kuma suka cinna masa wuta.

Ya ce a lokacin da ’yan sanda suka isa wurin mutumin ya riga ya kone, da suka dauke shi suka garzaya da shi Babban Asibitin Wudil, likitan ya tabbatar da cewa ya mutu.

Ya ce Rundunar ta fara bincike a kan lamarin.