✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen gari sun kone ’yan bindiga 3 kurmus a Katsina

Garuruwan dake yankin ne dai suka zauna a cikin shirin ko-ta-kwana bayan samun rahoton yunkurin kawo harin.

Wasu fusatattun mutane a garin Magamar Jibiya dake Karamar Hukumar Jibiya a jihar Katsina sun kashe tare da kone wasu ’yan bindigar uku kurmus a daidai lokacin da suka shiga yankin da nufin kai hari.

Lamarin dai ya faru ne ranar Lahadi da misalin karfe 11:25 na dare, a daidai lokacin da ’yan bindigar suka shiga garin da nufin kai hari.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa Aminiya cewa ’yan bindigar sun gamu da azal din ne lokacin da suka kutsa kai cikin gidan wani mutum ne, wanda shi kuma ya kwarmata musu ihu, lamarin da ya jawo hankulan ragowar mutanen gari wadanda su kuma suka yi musu kofar rago.

A cewar wani shugaban al’umma a yankin wanda bai amince a bayyana sunansa ba, tun da farko sun sami wani rahoton sirri ne cewa ’yan bindigar na kokarin kawo hari yankin, lamarin da ya sa dukkan garuruwan dake da makwabtaka da su suka yi shirin ko-ta-kwana.

“Naga gawarwakin biyu daga cikin ’yan bindigar wadanda aka kone su kurmus sannan aka jefar da su a Magama, amma na ukun kuwa wanda rahotanni suka ce yana sanye da kakin sojoji shi ’yan sanda ne suka tafi da gawarshi,” inji shi.

To sai dai Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Katsina, SP Gambo Isah bai tabbatar da faruwar lamarin ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Karamar Hukumar Jibiya dai na daya daga cikin Kananan Hukumomin jihar Katsina da ayyukan ’yan bindigar ya fi yi wa mummunar ta’asa.