✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen Jos na tururuwar zuwa kasuwanni bayan sassauta dokar hana fita

Mutane dai sun rika tururuwa zuwa kasuwanni da bankuna.

Mutanen birnin Jos na Jihar Filato na tururuwar zuwa kasuwanni domin sayen kayan amfanin yau da kullum bayan sassauta dokar hana fita da Gwamnatin Jihar ta yi.

A ranar Litinin ne dai Gwamnan Jihar, Simon Lalong ya sanar da sassauta dokar a wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar.

Yanzu haka dai dokar ta koma tsakanin karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.

Wakilinmu ya rawaito cewa jama’a na kuma tururuwar zuwa bankuna domin cirar kudi.

Wakilin Aminiya da ya zaga sassa da dama na birnin ya rawaito cewa manyan shaguna da sauran cibiyoyin kasuwanci sun bude domin had-hada.

Kazalika, manya da kananan tashoshin mota su ma sun ci gaba da aiki.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu wata barazana ga zaman lafiya a Jihar yayin da aka jibge jami’an tsaro a muhimman wurare na birnin.