✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mutanen Najeriya za su yaba wa Buhari a karshen mulkinsa’

Hatta masu adawa da gwamnatin Buhari za su yaba masa a karshen wa'adin mulkinsa.

Fadar Gwamnatin Najeriya ta ce wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari da zai cika nan da shekaru biyu masu zuwa, zai karkare ne da tarin yabo da jinjina gami da fatan alheri hatta daga masu adawa da gwamnatinsa.

Fadar Gwamnatin Najeriya ta sanar cewa, a yayin da wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari zai dasa aya nan da shekaru biyu masu zuwa, jama’ar kasar nan za su fahimci alheran da ya shuka musu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar a kan ayyuka da nasarorin da Gwamnatin Buhari ta samu tsawon shekaru shida da suka gabata.

Sanarwar mai taken ‘Gwamnatin Buhari bayan shekara shida: Kidaya Alheranta daya bayan daya’, ta ce jama’ar kasar nan za su rika kwarara yabo a garesa hatta daga ’yan adawa yayin da ya kammala wa’adin mulkinsa.

Adesina ya ce, “gwamnatin Buhari ta samu manyan nasarori a fannonin tattalin arziki da dama wanda hatta masu adawa za su yaba ba tare da son kai ko akidar siyayasa ta rufe musu idanu ba.

A yayin da a ranar 29 ga watan Mayun 2021 Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke cika shekara shida, nasarorin da ta samu za su bude kofar yin nazari a kan tasirin hakan wajen inganta rayuwar al’umma da kuma bunkasar Najeriya.

“Tun daga ababen more rayuwa zuwa tattalin ariki, ilimi, kiwon lafiya, wasanni, yaki da rashawa, ci gaban al’umma, alakar kasashen waje da sauransu, gwamnatin ta samu nasarori da dama da su kadai sun isa zama abun alfahari ga ’yan Najeriya.

“Musamman wadanda basu bari gurbataccen ra’ayi ko akidar siyasa ta yi wa zukatansu lullubi ba.

“Wasu na cewa, babu abin da su ji ko su gani gwamnatin ta tsinana, amma su bari idan wa’adin mulkin shugaba Buhari ya zo karshe za su fahimci irin alherin da ya shuka a kasar ta yadda hatta masu adawa da shi za su yaba masa.

“Ita gaskiya a kullum a bayyane take,” inji Adesina.