✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 1 ya rasu, 70 sun bace bayan ruftawar wurin hakar ma’adinai a Myanmar

Mutum 25 sun jikkata, wasu 70 kuma sun bace a bayan zaftarewar kasa a wurin hakar duwatsu masu daraja

Mutum daya ya rasu, 25 sun jikkata, wasu 70 kuma sun bace a sakamakon zaftarewar kasa a wurin hakar duwatsu masu daraja a kasar Myanmar.

Lamarin na ranar Laraba ya faru ne a Arewacin kasar, wadda a duk shekara mutane ke mutuwa a wuraren hakar duwatsu masu daraja.

Wani ma’aikacin ceto a wurin da abin ya faru, Ko Nyi, ya ce, “Yanzu haka mun kai mutum 25 asibiti, mun tsinci gawa daya sannan ba a ga mutum 70 zuwa 100 ba,” bayan faruwar abin da misalin karfe 4 na asuba (agogon kasar).

Hukumar Kashe Gobara ta Kasar Myanmar ta ce jami’anta da ke garin Hpakant inda abin ya faru da kuma Lone Khin mai makwabtaka da shi ne ke gudanar da aikin ceton, amma ba ta bayar da alkaluma ba.

Kasar ta zaftare ne wurin hakar duwatsu masu daraja na biliyoyin Dala a yankuna masu tsaunuka da ke garin Hpakant na Jihar Kachin da ke kusa da iyakar Myanmar da China.

Bangaren hakar duwatsu masu daraja na Myanmar na samun makudan kudade, sai dai babu isassun dokokin kula da bangaren, wanda ya dogara da leburori ’yan ci-rani da ake biya abin da bai taka kara ya karya ba, su hako duwatsun.

Wani mai fafutuka a kasar ya ce duk da gwamnatin sojin kasar ta haramta hakar ma’adinai zuwa watan Maris na 2022, a cikin damina daruruwan ma’aikatan hakar ma’adinai suka koma Hpakant domin ci gaba aiki.

Ya “A cikin dare suke fasa kasa, da safiya sai su fito da kasar ko duwatsun,” wanda nauyin kasar da duwatsun da aka hako ne ya sa wurin ya zaftare har zuwa tafkin da ke kusa da wurin.

M’aaikata kimanin 200 ne ke aikin ceto a wurin da abin ya faru, wadansu daga cikinsu na amfani da jiragen ruwa domin gano ko akwai gawarwaki a cikin tafkin da ke kusa da wurin.

Sojoji kasar sun sanya tsauraran matakan hana kaiwa ga wuraren hakar ma’adinai a yankin Arewacin kasar, wanda ba a samun intanet sosai.

Wata kungiyar yada labarai ta Kachin News Group ta ce a baya zaftarewar kasa ta kashe masu hakar ma’adinai 20.