Mutum 1 ya tsere yayin da ‘yan bindiga suka sace mutum 8 a Neja | Aminiya

Mutum 1 ya tsere yayin da ‘yan bindiga suka sace mutum 8 a Neja

‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga
    Abubakar Muhammad Usman Adam Umar

’Yan bindiga sun bi dare a unguwar Kwankwashe da ke kan hanyar Suleja zuwa Madalla a Jihar Neja, inda suka sace mutane ciki har da kananan yara.

Wani dan unguwar ya ce an sace wadanda abin ya rutsa da su ne daga gidaje uku da kuma wani otal da ke Unguwar Fulani a garin da misalin karfe 1 na dare, kafin wayewar garin Laraba.

  1. Mata ta sheka wa mijinta tafasasshen ruwa a Kano
  2. Mata ta sheka wa mijinta tafasasshen ruwa a Kano

Wata mata a garin, Faith Lucky, ta shaida mana cewa ’yan bindiga sun fasa gidanta sannan suka yi awon gaba da ’ya’yanta biyu, saurayi da budurwa.

“Na tashi ’ya’yan nawa daga barci sannan na lekawa ta taga in ga ’yan bindigar, amma cikin ’yan mintoci suka fasa tagar suka shigo.

“Sun kashe mana idanu da fitila mai hasken gaske, suka dora min bindiga, suka umarce ni da in bude kofar dakin,” inji matar.

SAURARI: Yadda yunwa ta sa likitoci yajin aiki:

Ta kara da cewa sai da maharan suka kwace musu wayoyinsu da kudaden da suke da su a hannunsu, kafin su tafi da ’ya’yan nata.

Ita kuma wata mata, cewa ta yi ’yan bindigar sun shiga harabar gidanta ne da misalin karfe 1 na dare, amma ita da mijinta sun samu sun tsere.

Ta ce maharan sun shiga sashin da mahaifiyarta da ta kawo musu ziyara da kuma ’yan uwan mijinta suke.

“Da suka shiga wurin mahaifiyata ba za ta iya motsawa ba, shi ya dan uwan mijina ya tsaya tare da ita, amma sun tafi da shi bayan sun kwashe mana wayoyi da kwamfuta sutura da takalma,” inji matar.

Wani mazaunin garin, mai suna Reuben, ya ce maharan sun shiga wani otal suka yi awon gaba da ma’aikatansa biyu.

Ya ce ’yan bindigar sun kwashe kusan awa guda suna tafka ta’asa kafin su tsere da suka ji harbin ’yan sanda.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Neja, ACP Sani Badarwa, amma lamarin ya ci tura.