✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ceto mutum 11 daga hannun masu garkuwa

Mutanen sun kubuta bayan sojoji sun ragargaji maboyan masu garkuwar.

Wasu mutum 11 daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su sun sun tsere daga hannun ’yan bindiga a Jihar Kaduna.

Mutanen sun tsere ne daga sansanin masu garkuwar da ke cikin adjin Sabon Birni daga ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar.

Gabanin nan, Aminiya ta kawo rahoton yadda wasu kanan yara ’yan gida ’yan kasa da shekara 11 suka kubuta daga hannun masu garkuwa bayan kwana 60 da sace su.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gidan Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar a ranar Alhamis cewa mutanen sun kubuta ne bayan wata ragargaza da sojoji suka yi wa sansanonin masu garkuwa a jihar.

A bayaninsa kan matakan da hukumomin tsaro ke dauka kan ayyukan ’yan bindiga a jihar, Aruwan ya ce, “Mutum 11 din da suka kubuta daga hannun masu garkuwa sun hada da wadanda aka sace su Karamar Hukumar Zariya da kuma kan Babbar Hanyar Kaduna zuwa Zariya”.

Daga cikin mutanen har da kananan yara biyar masu shekara biyar zuwa 10 sai kuma wata mata mai shai shayarwa da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a kan hanyarsu ta zuwa Ilorin daga Maiduguri.

A cewarsa, iyayen yaran sun biya kudin fansa Naira miliyan uku, amma masu garkuwar suka ki sakin su bisa hujjar cewa sai an kara musu da babur biyu.

Aruwan ya ce sojoji sun kuma kubutar da wata mata da aka yi garkwua da ita a Karamar Hukumar Lere, da wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su Karamar Hukumar Jema’a, an kuma mayar da ita ga iyalanta.

Ya ce Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya jinjina wa sojojin bisa namijin kokarin wajen ragargazar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da sauransu.