✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 11 sun mutu a hatsarin mota a Kano

Wani mummunan hatsarin mota a garin Kwanar Garko na karamar hukumar Garko ta jihar Kano ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 11.

Wani mummunan hatsarin mota a garin Kwanar Garko na karamar hukumar Garko ta jihar Kano ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 11.

Lamarin, wanda ya faru a kauyen Dakare dake kan hanyar Garko da misalin karfe 10:00 na safe ya rutsa da wata mota kirar Hayis da wata mai kirar Sharon.

Takwas daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su sun mutu nan take, yayin da ragowar ukun suka rasu a asibiti jim kadan da kai su domin samun agajin gaggawa.

Rahotanni sun ce yawancin wadanda hatsarin ya rutsa da su ‘yan kasuwa ne dake kan hanyarsu ta zuwa wata kasuwar kauye a garin Darki a karamar hukumar Wudil ta jihar Kano.

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa reshen jihar, Kabiru Daura ya ce mutum 20 ne hatsarin ya rutsa da su kuma shida daga ciki na cikin mawuyacin hali.