✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 11 sun mutu a hatsarin mota

Mutum 11 sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu suka samu rauni.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da mutuwar mutum 11 da hatsarin mota ya ritsa da su a kauyen Wuya da ke Karamar Hukumar Lemu ta Jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Adamu Usman, ya ce hatarin ya faru ne a ranar Asabar.

  1. Mahara sun kashe mutum 100 a Burkina Faso
  2. Soja ya kashe jami’in DSS saboda dan damfara

“Mutum 11 sun mutu a take, wadanda suka ji rauni kuma an kai su Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke garin Bida.

“Mun fara bincike sannan mun gargadi direbobi da su guji gudun wuce kima a yayin da suke tuki.”

Usman ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon faci da tayar motar ta yi, yayin da direban ke gudun ganganci.

Ya kara da cewa motar ta dauko babura 23 daga Jihar Katsina zuwa Jihar Legas, amma ’yan sanda ba su da tabbacin adadin mutanen da aka kwaso a cikin motar.