✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 11 sun mutu yayin turereniya a wajen rawa a Jamhuriyar Kwango

Daga cikin wadanda suka mutu har da 'yan sanda biyu

Akalla mutum ne 11 suka mutu yayin wata turereniya a wajen taron rawa da waka a babban filin wasa na Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.

Ministan Harkokin Cikin Gidan Kasar, Daniel Aselo Okito, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, inda ya zargi masu shirya sharholiyar da cunkusa adadin mutanen da suka haura wadanda ya kamata filin ya dauka.

Fitaccen mawakin nan dan kasar ta Kwango da ya shahara a kasashen Afirka da dama, Fally Ipupa, ne dai ya shirya taron.

Rahotanni sun ce mutane sama da 80,000 din da ya kamata filin ya dauka ne suka rika turereniyar shiga filin, ciki har da kutsa kansu wajen shigar manyan mutane.

“Mutum 11, cikinsu har da ’yan sanda biyu sun mutu,” inji Ministan, lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a filin tare da mika ta’aziyyarsa da iyalan mamatan.

Sai dai ya ce ya zama wajibi a hukunta wadanda suka shirya taron saboda yin kantafi da rayuwar masu kallo.

Mai shekara 44, mawaki Fally Ipupa dai na daya daga cikin manyan mawakan Afirka wadanda wakokinsa suka karade duk fadin duniya.

Mawakin dai ya isa wajen taron ne sa’o’i da dama bayan lokacin da aka tsara fara shi, a ranar da iftila’in zai faru.