✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 11 ’yan bindiga suka kashe a kasuwa a Filato

Cikin mutanen da aka kashe a kasuwar Pinau har da mata da kananan yara

Mutanen da suka rasu a sakamakon bude wuta da ’yan bindiga suka yi a yankin Pinau da ke Karamar Hukumar Wase ta Jihar Filato sun karu zuwa mutum 11.

Tun da farko Aminiya ta kawo rahoto cewa mutum bakwai ne suka rasu a harin da ’yan bindiga suka kai kasuwar a yayin da ake tsaka da gudanar da hadahadar cinikayya.

Daga bayan wani shugaban matasan yankin, Shafi’i Sambo, ya ce, “Yanzu mutum 11 ne suka rasu, takwas daga cikinsu maza ne, sai kuma mata da kanana yara.”

’Yan bindiga sun far wa kasuwar da ke unguwar Pinau da ka Karamar Hukumar Wase ta Jihar ne  ranar Lahadi.

Gabanin harin, a ranar Laraba 8 ga Disamba, 2021, mazauna wasu kauyuka a karamar hukumar sun yi korafin cewa ’yan bindiga na shigar yankunansu.

Sun kuma koka cewa masu hada baki da ’yan bindigar suna kawo cikas ga kokarin jami’an tsaro na magance matsalar.

Wata majiya a kauyen ta ce a kwana 10 da suka gabata ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da yawa a yankin kuma sun karbi miliyoyin kudade a matsayin kudin fansa.

Majiyar ta ce, “Miliyoyi suke karba a matsayin kudin fansa, wani lokacin Naira miliyan biyu, har zuwa miliyan biyar. Kwana uku da suka wuce sun karbi Naira miliyan biyar kafin suka sako wani mutum da suka yi garkuwa da shi.”

Wakilinmu a Jos ya nemi kakakin ’yan sandan Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, domin samun karin bayani, sai dai jami’in dan sandan bai amsa kiran wayan wakilin namu ko rubutaccen sakon da ya tura mishi ba.

An kai harin ne kwanaki kadan bayan wani kisan gilla da ’yan bindiga suka yi wa wasu matafiya da suka tare suka kuma sa musu wuta a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.