✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 110 sun mutu sakamakon ambaliya da zabtarewar kasa a Philippine

Ana ci gaba da neman wasu mutum 33 da suka bace, yayin da sama da mutum 100 sun jikkata.

Rahotanni daga Philippines sun nuna akalla mutum 110 sun mutu sannan sama da miliyan 2.4 sun shiga matsi sakamakon iftila’in ambaliyar ruwa da gocewar kasa da ta auku a kasar.

Hukumar kula da iftila’i ta kasar ta fada a ranar Talata cewa, ambaliya da gocewar kasar sun faru ne sakamakon mamakon ruwan sama.

A cewar hukumar, ana ci gaba da neman wasu mutum 33 da suka bace, yayin da sama da mutum 100 sun jikkata.

Ta kara da cewa, iftila’in ya lalata gidaje sama da 100 a yankin Magundanao da ke Kudancin kasar, kuma 59 daga cikin wadanda suka mutun daga yankin suke.

Kazalika, hukumar ta ce mutum 16 sun bace a Maguindanao, tare da cewa mawuyacin al’amari ne a gano masu sauran numafashi daga wadanda lamarin ya rutsa da su a yankin.

Sauran yankunan da lamarin ya shafa kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana sun hada da Yammacin Visayas da Cavite da Laguna da kuma Batangas.