✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 12 sun kone a hatsarin mota a Kano

Motocin sun kama da wuta sakamakon taho mu gama da juna.

Rahotanni sun nuna cewar mutum 12 ne suka kone kurmus a sanadin wani hatsarin mota da ya afku tsakanin wasu motocin haya biyu a babbar hanyar Kano zuwa Kaduna.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru da misalin karfe 3 na yammacin ranar Litinin a daidai garin Tsamawa da ke Karamar Hukumar Garun Malam, inda duk fasinjojin motocin biyu suka riga mu gidan gaskiya.

Da ya ke tabbatar da faruwar hatsarin ga Aminiya,Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf, ya ce sun samu kiran agaji daga wani mutum da ake kira Isa Maishayi.

Ya kara da cewar bayan isar su wajen da lamarin ya afku, tuni motocin sun kama da wuta, wanda hakan ya sa suka gane mutanen da ke ciki ko lambar motocin da suka yi hatsarin.

“Ranar Litinin 28 ga Fabrairu 2022, ofishinmu da ke Karamar Hukumar Kura ya samu kiran neman agajin gaggawa da misalin karfe 3 na yamma daga wani Isah Mai Fetur, wanda ya bayar da rahoton cewa hatsari ya afku a garin Tsamawa da ke Karamar Hukumar Garun Malam.

“Bayan isar jami’anmu sun riske ababen hawa biyu sun kama da wuta a kan hanyar Kano zuwa Kaduna.

“An yi kokarin ceto fasinjojin amma gaba dayansu sun kone, don haka ba za a iya gane shekarunsu ba,” a cewarsa.

Kakakin ya ce tuni jami’an hukumar kiyaye hadura (FRSC) suka dauke gawarwakin wanda suka rasu zuwa asibiti.

Sai dai Kwamandan hukumar reshen Jihar Kano, Mato Zubairu bai amsa kiran wayar da wakilinmu ya yi masa bare a ji ta bakinsa kan faruwar hatsarin.