✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 12 ’yan gida daya sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato

Jirgin ruwan ya kife da su a yayin da suke dawowa daga biki.

Mutum 12 ’yan gida daya sun rasu a hatsarin jirgin ruwa da ya nutse da su a kauyen Doruwa na Karamar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato.

Jirgin ruwan ya kife da maza da kananan yara da tsoffi 18, dukansu ’yan gida daya ne a hanyarsu ta komawa gida daga shagalin bikin da suka halarta a kauyen Ginga a Karamar Hukumar a ranar Alhamis.

Tuntsurewar da jirgin ruwan ya yi da fasinjoin ya auku ne a lokacin da suka kawo Bakin Ganga da marecen Alhamis, nan take aka fitar da mutum 13 aka yi masu sutura, aka kuma ci gaba da neman sauran mutum biyar.

“Mutum 12 ne suka rasu domin na 13 yaro ne, a makabarta ya farfado aka gano da ransa bai rasu ba, ina addu’ar Allah Ya gafarta musu,” inji dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar a Majalisar Dokokin Jiha, Maidawa Kajiji.

Dan majalisar ya ce mutum biyar sun tsira tare da direban jirgin da ya kife da mamatan a hanyarsu ta dawowa daga buki, inda suka hadu da ajalinsu.

Majiyarmu ta ce fasinjojin da jirgin ya kife da su din sun yi masa yawa, saboda a cewar majiyar, ta gan su kafin faduwar jirgin.

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya jajanta wa iyalan mamatan, ya kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta musu.

Tsohon Gwamnan na Sakkwato ya bayyana kaduwarsa da lamarin, a yayin da yake mika ta’aziya ga mutanen Karamar Hukumar Shagari da Jihar ta Sakkwato baki daya.