✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 13 sun rasu a hatsarin mota a Katsina

Da dama sun jikkata, dabbobi 70 sun mutu a hanyar Kaita-Dankama

Akalla mutum 13 sun rasu, wasu da dama kuma suka masu munanan raunuka a hatsarin da ya ritsa da wata tirela a hanyar Kaita zuwa Dankama a Jihar Katsina.

Hatsarin ya auku ne a yayin da babbar motar dabbobin kirar Iveco da ta dauko mutanen ta kama hanyar zuwa Legas a daren Alhamis.

Shaidu sun ce gudun wuce ka’ida ne ya yi sanadiyyar kwacewar motar da ta fadi bayan barowarta Kasuwar kan iyaka da ke Dankama, nan take kuma dabbobi 70 suka hallaka.

Sun ce an garzaya da gawarwakin Babban Asibitin Katsina, inda dangi suka dauke su aka yi musu sutura; mutum shida daga Jamhuriyar Nijar daga cikinsu kuma ’yan uwansu ba su samu daukar su ba.

Mataimakin Shugaban ’Yan Kasuwar Dabbobi na Jamhuriyar Nijar a Jihar, ya bayyana kaduwarsa da rashin da aka yi, inda ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Katsina da ta dauki nauyi kula da wadanda suka samu rauni da kuma jana’izar mamatan.

Gwamnatin Jihar Katsina ta tura jami’anta sun halarci jana’izar mamatan su shida ’yan Jamhuriyar da aka yi wa sutura a Makabartar Dan Takum da ke garin Katsina, wanda Imam Yahaya Haruna ya jarogaranta.

Tawagar Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Kwamishinan Kakanan Hukumomi, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo ta yi wa iyalan mamatan ta’aziyya tare da addu’ar samun rahama gare su.

Ya kuma yi addu’ar samun sauki ga wadanda suka samu raunuka da ke kwance a Babban Asibitin Katsina, Babbar Cibiyar Lafiya ta Tarayya da kuma Asibitin Kashi na Amadi Rimi.