✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 13 ’yan bindiga suka kashe a Neja —’Yan sanda

Har yanzu ba a samu cikakken bayani ba saboda yanayin dazuzzukan da kauyukan ke ciki.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Neja ta tabbatar da mutuwar mutane akalla 13 a wasu kauyukan Neja guda biyu da ke Karamar Hukumar Shiroro. 

Rundunar ta ce an kashe mutanen kauyen ne a lokacin da suke aikin girbin amfanin gona a kauyukan Nukundna da Wurukuchi a ranar Talata.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce “har yanzu ba a samu cikakken bayanin harin ba saboda yanayin dazuzzukan da kauyukan ke ciki”.

Muryar Amurka ta ruwaito Abiodun yana cewa jami’in ‘yan sanda na yankin ne ya jagoranci rundunar ‘yan sandan inda za su fara farautar ‘yan bindigar.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa ‘yan sanda za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa amma ya nemi a ba su bayanan da za su kai ga cafke ‘yan bindigan.

A wani rahoton da jaridar Premium Times ta wallafa, ya kara tabbatar da cewa mutane 13 aka kashe a harin sabanin 37 da wasu kafofin watsa labaran suka ruwaito.

Wasu rahotani na cewa an kona wasu gidaje daya daga cikin kauyukan gabaki daya wanda hakan ya sanya wasu daga cikin mutanen kauyen suka nemi masauki da matsuguni a Kuta, hedikwatar karamar hukumar.